Shugaba Buhari Ya Umurci Hafsoshin Tsaro Su Tabbatar Da Hadinkan Kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da manyan hafsoshin tsaro yayin da ya umurce su da kasa su yi kasa a gwiwa wajen tabbatar da hadinkan kasar nan.
An yi ganawar ta tsawon sa’o’i uku ce a gidan da shugaba Buharin ke zaune a fadar Aso Rock da ke Abuja.
Shugaban kasan ya umurci hafsoshin tsaron da su tashi tsaye har sai sunga abun da ya turewa buzu nadi, musamman idan suka yi la’akari da jawabinsa na ranar Litinin inda ya ce ba za a yi rikon sakaina… ga hadin kasa ba.
Har ila yau, ya bukaci hafsoshin tsaron da su tabbatar da ganin sun kare rayuka da dukiyayoyin ‘yan Najeriya.
A lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa, hafsan hafsoshin tsaron, Janar Olanishakin ya ce sun kwashe sa’o’i uku suna ganawa da shugaban kasa a kan batutuwan da suka shafi tsaro a ciki da wajen Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *