Majalisar dinkin duniya ta tabbatar da mutuwar mutane 23 sanadiyar annobar amai da gudawa a Maiduguri

Majalisar dinkin duniya ta tabbatar da mutuwar mutane ashirin da uku sakamakon barkewar annobar amai da gudawa, yayin da mutum dari biyar da talati da uku yanzu haka ke fama da cutar.

Hukumar jin kai ta majalisar dinkin duniya a Maiduguri ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar, biyo bayan rahoton da ta samu daga ma’aikatar lafiya ta jihar Borno.

Sanarwar ta ce annobar an samu rahoton bullar annobar amai da gudawa a kananan hukumomin Manguno da Dikwa, da kuma kudu maso gabashi da kuma gabashin birnin Maiduguri.

Hukumar jin kan tace yawan kididdigar da ake samu na masu kamuwa da cutar na bukatar agajin gaggawa, la’akari da cewa cutar wata babbar barazana ce.

Sanarwar ta kara da cewa  yanzu haka ma’aikatar lafiya ta jihar Borno tare da hukumar kula da Tsaftar muhalli da ruwa da kungiyoyin bada agaji da suka hadar da hukumomin majalisa dinkin duniya a jihar na cigaba da kula da masu fama da cutar, tare da lalubo hanyoyin dakile yaduwar annobar.

Hukumar jin kan ta majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa yanzu haka an kafa wasu cibiyoyin bada agajin gaggawa, inda kuma aka ajiye gadojin kula da masu fama da cutar amai da gudawan a sansanin ‘yan gudun hijira na Muna tare da taimakon jami’an jin kai domin basu kulawar gaggawa.

 

 

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *