Hadaddiyar kungiyar likitoci ta kasa ta janye yajin aikin sai baba ta gani

Hadaddiyar kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta kasa ta ki janye yajin aikin gama gari da ‘ya’yan kungiyar suka fara a satin nan da muke ciki.

‘ya’yan kungiyar dai sun ki janye yajin aikin duk kuwa da zaman tattaunawar da aka yi da su na tsawon awanni 13 da aka yi a daren jiya tsakanin su da wasu wakilan gwamnatin tarayya a sakatariyar gwamnatin tarayya da ke Abuja.

Zaman tattaunawar wanda aka karkare shi da asubahin yau an yi shi ne karkashin jagorancin ministan ayyuka Chris Ngige da ministan lafiya Farfesa Isaac Adewole, da kuma karamin ministan lafiya Dr. Osagie Ehanire.

Sai dai ministan ayyuka na kasa ya ruwaito cewa ana sa ran yajin aikinzai kare ne a gobe juma’a inda za’ mika bukatun  likitocin ga gwamnati wadanda suka hadar da na biyan albashin su da ariya da suke bin gwamnati da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *