Kungiyar kare hakki, hadin kai ta bukaci da a sauya karatun almajirci zuwa na zamani

Kungiyar kare hakki, hadin kai da zaman lafiya ta matasan arewa tayi kira ga gwamnatin tarayya, da ta sauya tsarin karantun almajiranci zuwa karatun zamani.

Shugaban kungiyar na kasa kwamred Muhammad Haruna Gaza ne yayi wannan kiran cikin wata sanarwa ya fitar jiya a nan Kano, inda ya ce ya kamata gwamnatin tarayya ta inganta karatun Almajirai ta hanyar koyar da su karatun zamani da na addini a makarantu daban-daban da ke fadin kasar nan.

Kwamred Haruna Gaza ya kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta hada kai da manyan shugabannin addinin Islama wajen kafa kwamitin da zai taimaka wajen bullo da hanyoyin da za’a bi wajen inganta rayuwar almajiran.

Sanarwar ta bayyana cewa idan har aka bullo da wannan tsarin zai taimakawa wajen inganta ilimin yara Almajirai, musamman ma idan aka basu damar samun takardun shaidar gama matakin Diploma, digiri da dai sauran su.

Sanarwar mai dauke da sa hannun Sakataren kungiyar na kasa Kwamred Abdulhadi Garba Rabiu ta ruwaito shugaban kungiyar na cewa matakin zai taimaka dakile yawon barace-baracen da almajiran keyi a tituna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *