‘KARANCIN KUDI NA HANA NAJERIYA AIWATAR DA MANYAN AYYUKA’

Ministan kasafin kudi da tsare-tsare n kasa, Sanata Udoma Udo Udoma ya ce karancin kudi ne babbar matsalar da gwamnatin tarayya ke fama da ita wajen aiwatar da kasafin kudinta.

A lokacin da ya ke gabatar da jawabi a wajen taron ganawa da al’umma a kan kasafin kudin shekarar 2018 wanda aka yi a Abuja a ranar Talata, ministan ya sheda wa masu ruwa da tsaki cewa gwamnati na samun tarnaki wajen aiwatar da manyan ayyuka ne, saboda karancin kudaden shiga.

A cewarsa, galibin manyan ayyukan da ke kunshe a cikin kasafin kudin shekarar 2017 za su shiga cikin shekarar 2018, saboda karancin kudi da aka fuskanta a shekarar 2017, yana mai cewa kasafin kudin bana ya dogara ne a kan bashi daga kasashen ketare.

Sanata Udoma ya cigaba da cewa Naira miliyan dubu dari da hamsin da aka saki a ranar talatin da daya ga watan Oktoban wannan shekarar na wasu ayyuka ne da ake bukatar yi a cikin wata hudu na wannan shekara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *