‘BA ZA A TURA MASU YI WA KASA HIDIMA ZUWA YANKUNA MASU MATSALAR TSARO BA’

Babban daraktan hukumar kula da matasa masu yi wa kasa hidima-NYSC, Birgediya Janar Suleman Kazaure ya tabbatar wa masu yi wa kasa hidima cewa babu wanda za a tura zuwa yankunan da ake da matsalolin tsaro.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai rikon mukamin Daraktan kula da hulda da jama’a na hukumar, Misis Adenike Adeyemi ta ce Kazaure ya bayyana haka ne a sansanin matasa masu yi wa kasa hidima da ke Tsafe a jihar Zamfara da kuma na jihar Sakkwato da ke karamar hukumar Wamakko.

Ya ce tsaron rayukan matasa masu bauta wa kasa ne babban burin hukumar NYSC.

Janar Kazaure ya bukaci masu yi wa kasa hidama da su koyi sana’o’in hannu yayin da su ke sansani, domin ganin sun kaucewa shiga jerin masu zaman kashe wando a lokacin da suka kammala aikin bautawa kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *