TSOFAFFIN DALIBAN KWALEJIN GWAMNATI TA FUNTUA SUN KAI WA KWALEJIN DAUKI

Mai shara’a Musa Danladi Abubakar na sashen shara’a a jihar Katsina ya yi kira ga daliban kwalejin gwamnati da ke Funtua da su sadaukar da kai wajen cimma manufofin kwalejin.

Ya yi wannan kira ne a wajen bikin  shekara na kwalejin karo na arba’in ‘yan ajin shekarar 1977 wanda aka yi a Funtua a karshen mako.

Mai shara’a Abubakar wanda shi ne shugaban taron, ya jaddada cewa gwamnatin jihar Katsina kadai ba za ta iya magance dukkan matsalolin kwalejin ba, dan haka wajibi ne tsofaffin dalibai su kai nasu daukin.

A wajen bikin dai, tsofaffin daliban na ajin shekarar 1977 sun ba da gudumawar wasu kayayyaki ga kwalejin, kana sun bada gudunmawa ga iyalan mambobin kungiyar wadanda suka riga mu gidan gaskiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *